Wata rana Elisha ya wuce zuwa Shunem inda wata mace take da zama, sai ta gayyace shi cin abinci. Don haka duk lokacin da ya bi ta wannan hanya, sai ya ratsa ta gidanta, ya ci abinci.
Amma sarki Yehoram ya komo Yezreyel, don ya yi jiyyar raunukan da Suriyawa suka yi masa sa'ad da ya yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Yehu ya ce, “Idan wannan shi ne nufinku, to, kada kowa ya zurare, ya tafi, ya ba da labari a Yezreyel.”
Sai sarki Yehoram ya koma zuwa Yezreyel don ya yi jiyyar raunukan da Suriyawa suka yi masa sa'ad da yake yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Ahaziya, ɗan Yoram, Sarkin Yahuza ya tafi ya ziyarci Yehoram ɗan Ahab cikin Yezreyel saboda yana ciwo.
Ta ce masa, “To, sai ka faɗa.” Sai ya ce, “In kin yarda ki yi magana da sarki Sulemanu, gama ba zai ƙi jinki ba, ki ce ya ba ni yarinyar nan, Abishag, daga Shunem, ta zama matata.”
Sai mutanen kabilan Yusufu suka ce, “Ƙasar tuddai ba ta ishe mu ba, ga kuma Kan'aniyawa da suke zaune a filin, da waɗanda suke a Bet-sheyan da ƙauyukanta, da waɗanda suke cikin Kwarin Yezreyel suna da karusan ƙarfe.”