Ya kuma aika zuwa ga Kan'aniyawan da suke gabas da yamma, da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa da suke ƙasar tuddai, da Hiwiyawa da suke zaune a gindin Dutsen Harmon a ƙasar Mizfa.
Sa'ad da shugabannin mayaƙa su da mayaƙansu suka ji Sarkin Babila ya naɗa Gedaliya ya zama hakimi, sai suka zo tare da mutanensu wurin Gedaliya a Mizfa, wato su Isma'ilu ɗan Netaniya, da Yohenan ɗan Kareya, da Seraiya ɗan Tanhumet, mutumin Netofa, da Yazaniya mutumin Ma'aka.
Dukan jama'ar Isra'ila fa suka fito tun daga Dan a arewa har zuwa Biyer-sheba a kudu da kuma Gileyad daga gabas. Suka hallara gaba ɗaya a gaban Ubangiji a Mizfa.
Isra'ilawa fa suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa, suka zuba a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a ranan nan, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi.” Sama'ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra'ilawa.
Shi ɗan nan na Saul yana da shugabanni biyu na 'yan hari, su ne Ba'ana da Rekab, 'ya'yan Rimmon na ƙasar Biliyaminu daga Biyerot, (gama an lasafta Biyerot cikin yankin ƙasar Biliyaminu.
Sa'an nan sarki Asa ya gayyaci dukan jama'ar Yahuza, ba wanda aka ɗauke wa. Suka tafi suka kwashe duwatsu da katakai waɗanda Ba'asha yake ginin Rama da su. Da su sarki Asa ya gina Geba ta Biliyaminu, da Mizfa.