Ubangiji zai yi yaƙi kamar yadda ya yi a Dutsen Ferazim da a Kwarin Gibeyon domin ya aikata abin da ya yi nufin yi, ko da yake ayyukansa suna da ban al'ajabi. Zai gama aikinsa, wannan aiki kuwa mai ban al'ajabi ne.
Akwai wani mutum daga kabilar Ifraimu sunansa Elkana, yana zaune a Rama, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Shi ɗan Yeroham ne, jika ga Eliyab, na iyalin Nahat, daga zuriyar Zuf.
Shi ɗan nan na Saul yana da shugabanni biyu na 'yan hari, su ne Ba'ana da Rekab, 'ya'yan Rimmon na ƙasar Biliyaminu daga Biyerot, (gama an lasafta Biyerot cikin yankin ƙasar Biliyaminu.
Elkana da iyalinsa suka tashi tun da sassafe suka yi wa Ubangiji sujada, sa'an nan suka koma gidansu a Rama. Elkana fa ya kwana da matarsa, Hannatu. Ubangiji kuwa ya tuna da ita.