Ta kuma kewaye kudancin Ba'ala zuwa Dutsen Seyir. Ta zarce zuwa arewacin kafaɗar Dutsen Yeyarim, wato Kesalon. Daga nan ta gangara zuwa Bet-shemesh, ta kuma wuce zuwa Timna.
A kwana a tashi, ga matar Yahuza, 'yar Shuwa ta rasu. Da Yahuza ya gama karɓar ta'aziyya, sai ya haura Timna wurin masu sausayar tumakinsa, da shi da abokinsa Hira Ba'adullame.