Don haka sai ya koma Yezreyel don ya yi jiyyar raunukan da aka yi masa a Rama, sa'ad da suka yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Ahaziya ɗan Yoram, Sarkin Yahuza, ya gangara don ya gai da Yehoram ɗan Ahab a Yezreyel wanda yake rashin lafiya.
Sai mutanen kabilan Yusufu suka ce, “Ƙasar tuddai ba ta ishe mu ba, ga kuma Kan'aniyawa da suke zaune a filin, da waɗanda suke a Bet-sheyan da ƙauyukanta, da waɗanda suke cikin Kwarin Yezreyel suna da karusan ƙarfe.”
Hanun da mazaunan Zanowa suka gyara Ƙofar Kwari. Sun gina ta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta, da ƙyamarenta, suka gyara garun kamu dubu, har zuwa Ƙofar Juji.