Akwai wani mutumin Mawon wanda yake da harka a Karmel. Mutumin mai dukiya ne ƙwarai, yana da tumaki dubu uku (3,000) da awaki dubu (1,000). Yana yi wa tumakinsa sausaya a Karmel.
Saul da mutanensa suka tafi neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya sauka daga dutsen ya zauna a can jejin Mawon. Da Saul ya ji, sai ya bi Dawuda zuwa jejin Mawon.
Hamada za ta raira waƙa da sowa don murna, Za ta zama kyakkyawa kamar Dutsen Lebanon, Da dausayi kamar filayen Karmel da Sharon. Kowa zai ga mafificiyar ɗaukakar Allah, Ya ga girmansa da ikonsa.
Ya kuma gina hasumiyai a jeji, ya haƙa tafukka masu yawa, saboda yana da garkunan dabbobi da yawa, da waɗanda suke Shefela da waɗanda suke a filin tudu. Yana kuma da manoma da masu yi wa kurangar inabi aski a tuddai, da wajen ƙasashe masu dausayi, gama shi mai son noma ne ƙwarai.
da Ayin tare da wuraren kiwo nata, da Yutta tare da wuraren kiwo nata, da Bet-shemesh tare da wuraren kiwo nata. Birane tara ke nan daga cikin kabilun nan biyu.
Sa'an nan ya tashi tun da sassafe domin ya sadu da Saul. Aka faɗa wa Sama'ila, Saul ya tafi Karmel, ya kafa wa kansa al'amudi, sa'an nan ya juya ya wuce zuwa Gilgal.