Ta haka kuwa Joshuwa ya ci ƙasan nan duka, da ƙasar tuddai, da Negeb duka, da dukan ƙasar Goshen, da filayen kwari, da Araba, da ƙasar tuddai ta Isra'ila da filayen kwarinta,
Lokacin da Absalom yake miƙa hadaya, sai ya aika zuwa Gilo a kira masa Ahitofel Bagilone mai ba Dawuda shawara. Maƙarƙashiyar kuwa ta yi ƙarfi. Mutane masu haɗa kai da Absalom suka riƙa ƙaruwa kullum.