46 Daga Ekron zuwa tekun, da dukan garuruwa da ƙauyukan da suke kusa da Ashdod.
46 yammancin Ekron da dukan garuruwa da ƙauyukan da suke kusa da Ashdod.
Zan kawar da masu sarautar biranen Ashdod da Ashkelon, Zan karɓe sandan mulkin Ekron. Sauran Filistiyawa da suka ragu kuma, Za su mutu duka.”
Bisa ga umarnin Sargon, Sarkin Assuriya, sai sarkin yaƙin Assuriya ya fāɗa wa Ashdod, birnin Filistiyawa, da yaƙi.
Azariya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Filistiyawa, ya rushe garun Gat, da na Yamniya, da na Ashdod. Ya giggina birane a ƙasar Ashdod, da waɗansu wurare na Filistiyawa.
Ubangiji kuwa ya hukunta mutanen Ashdod ƙwarai da gaske, ya kuma razanar da su, ya azabtar da su da marurai, su da na kewaye da su.
Sa'ad da Filistiyawa suka ƙwace akwatin alkawarin Allah a Ebenezer, suka kai shi Ashdod.
Babu wani gwarzon da ya ragu a ƙasar mutanen Isra'ila, sai a Gaza, da Gat, da Ashdod kaɗai ne waɗansunsu suka ragu.
Da kuma Ekron da garuruwanta da ƙauyukanta.
Ashdod da garuruwanta da ƙauyukanta, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta zuwa rafin Masar da Bahar Rum da bakinta.