'Yan'uwansa da dukan danginsa, suka gangara, suka ɗauki gawarsa, suka binne a kabarin Zora da Eshtawol. Samson ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin.
Da suka isa Kwarin Eshkol, sai suka datse reshe guda na nonon inabi da 'ya'ya cunkus. Suka rataya a sanda, mutum biyu suka ɗauka a kafaɗunsu. Suka kuma kawo rumman da ɓaure.
da iyalan da suke a Kiriyat-yeyarim, da na Itiriyawa, da na Futiyawa, da na Shumatiyawa, da na Mishraiyawa. Daga waɗannan ne Zoratiyawa da Eshtawoliyawa suka fito.