Sa'ad da Dawuda da mutanensa suka koma Ziklag a rana ta uku, sai suka tarar Amalekawa sun riga sun kawo wa Negeb da Ziklag hari. Suka cinye Ziklag, suka ƙone ta.
Mutane da yawa suka haɗa kai da Dawuda lokacin da yake a Ziklag, sa'ad da yake a takure saboda Saul ɗan Kish. Su ma suna cikin manyan jarumawan da suka taimake shi yaƙi. Dukansu gwanayen sojoji ne, suna iya su harba kibiya, ko su yi jifa da majajjawa da hannun dama ko da na hagu.