20 Wannan shi ne gādon jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu.
20 Wannan shi ne gādon kabilar Yahuda bisa ga iyalansu.
A kan Yahuza ya ce, “Ka ji muryar Yahuza, ya Ubangiji, Ka kawo shi wurin jama'arsa. Ka yi yaƙi da ikonka dominsu, Ka taimake shi a kan maƙiyansa.”
Ta kuwa ce masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ina roƙonka ka ba ni maɓuɓɓugar ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugar tuddai da na kwari.
Biranen jama'ar Yahuza da suke can kudu sosai wajen iyakar Edom, su ne Kabzeyel, da Eder, da Yagur,