Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 14:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Kabilan nan tara da rabi sun karɓi nasu rabon gādo ta hanyar jefa kuri'a, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Ta wurin yin ƙuri’a aka raba wa kabilan nan tara da rabi, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 14:2
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Musa ya ce wa Isra'ilawa, “Wannan ita ce ƙasar da za ku gāda ta hanyar jefa kuri'a. Ƙasar da Ubangiji ya umarta a ba kabilai tara da rabi.


Za ku rarraba wa kanku gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar jefar kuri'a. Za ku ba babbar kabila babban rabo, ƙaramar kabila kuwa ku ba ta ƙaramin rabo. Inda duk kuri'a ta fāɗa wa mutum, nan ne zai zama wurinsa. Bisa ga kabilan kakanninku za ku gāji ƙasar.


Mutane sukan jefa kuri'a don su san nufin Allah, amma Allah da kansa ne yake ba da amsa.


Sa'an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.


Idan mutum biyu ƙarfafa suna jayayya da juna a gaban shari'a, kuri'a a asirce kaɗai take iya daidaita tsakaninsu.


Sai suka yi musu kuri'a, Matiyas ya ci, aka kuma sa shi a cikin manzannin nan goma sha ɗaya.


“Ga sunayen mutanen da za su taimake ka raba gādon ƙasar, Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun.


Ku auna ƙasar, ku raba ta kashi bakwai, sa'an nan ku kawo mini taswirar ƙasar. Ni kuwa zan jefa muku kuri'a a gaban Ubangiji Allahnmu.


Yanzu fa sai ka raba wa kabilai tara da rabi ɗin nan ƙasar ta zama gādonsu.”


Joshuwa kuwa ya jefa musu kuri'a a gaban Ubangiji a Shilo. Ta haka ya rarraba ƙasar ga jama'ar Isra'ila, kowa ya sami rabonsa.


“Sa'ad da kuka rarraba ƙasar gādo, sai ku keɓe wa Ubangiji wani wuri domin ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), faɗinsa kuwa kamu dubu goma (10,000). Dukan yankin zai zama wuri mai tsarki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ