Kamar yadda Ubangiji ya umarci Joshuwa, ya ba Kalibu, ɗan Yefunne, rabonsa a tsakiyar jama'ar Yahuza. Rabon da aka ba shi, shi ne Kiriyat-arba, wato Hebron. Arba shi ne uban Anak.
Amma ɗaya kaɗai nake ƙauna, Ita kyakkyawa ce kamar kurciya. Tilo ce ga mahaifiyarta, 'yar lele ce ga mahaifiyarta. Mata duk sukan dube ta, su yaba. Matan sarki da ƙwaraƙwaransa suka raira waƙa suka yabe ta.
Bayan wannan sai Dawuda ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ko in haura in mallaki ɗaya daga cikin garuruwan Yahuza?” Ubangiji ya ce masa, “Ka haura.” Dawuda kuma ya ce, “Zuwa wane gari zan haura?” Sai Ubangiji ya ce masa, “Zuwa Hebron.”