Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 13:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, sun karɓi nasu gādo wanda Musa ya ba su a hayin Urdun wajen gabas. Abin da Musa, bawan Ubangiji, ya ba su ke nan,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Rabin kabilar Manasse, mutanen Ruben da mutanen Gad suka karɓi rabonsu na gādo wanda Musa ya ba su a gabashin Urdun. Abin da Musa bawan Ubangiji ya ba su ke nan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 13:8
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Musa, bawan Ubangiji, da Isra'ilawa suka ci sarakunan nan da yaƙi, sa'an nan ya ba da ƙasarsu ga Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa.


Yanzu Ubangiji Allahnku ya ba 'yan'uwanku hutawa kamar yadda ya faɗa, yanzu dai sai ku koma, ku tafi gida a ƙasarku ta gādo wadda Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun.


Mutanen Ra'ubainu, da na Gad, da rabin kabilar Manassa kuwa suka haye tare da 'yan'uwansu da shirin yaƙi kamar yadda Musa ya umarce su.


Gama ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayi na gabashin Urdun.”


“A lokacin ne fa muka ƙwace wannan ƙasa daga hannun sarakunan nan biyu na Amoriyawa, wato ƙasa wadda take a hayin Urdun, daga kwarin kogin Arnon zuwa Dutsen Harmon.”


Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Isra'ilawa suka cinye da yaƙi, suka mallaki ƙasarsu a hayin Kogin Urdun daga yamma, tun daga kwarin Arnon har zuwa Dutsen Harmon da dukan Araba a wajen gabas,


Yanzu fa sai ka raba wa kabilai tara da rabi ɗin nan ƙasar ta zama gādonsu.”


daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu ta Medeba zuwa Dibon,


Waɗansu kuwa suka haye Kogin Urdun zuwa ƙasar Gad da Gileyad. Saul kuwa yana can a Gilgal. Dukan mutanen da suka bi shi suka yi ta rawar jiki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ