Za ku rarraba wa kanku gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar jefar kuri'a. Za ku ba babbar kabila babban rabo, ƙaramar kabila kuwa ku ba ta ƙaramin rabo. Inda duk kuri'a ta fāɗa wa mutum, nan ne zai zama wurinsa. Bisa ga kabilan kakanninku za ku gāji ƙasar.
da dukan mazaunan ƙasar tuddai, tun daga Lebanon zuwa Misrefot-mayim har da dukan Sidoniyawa. Ni da kaina zan kore su a gaban jama'ar Isra'ila. Kai kuwa za ka raba wa Isra'ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka.
Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, sun karɓi nasu gādo wanda Musa ya ba su a hayin Urdun wajen gabas. Abin da Musa, bawan Ubangiji, ya ba su ke nan,
Ya kori mazaunan wurin sa'ad da jama'arsa suka dirkako, Ya rarraba ƙasar ga kabilan Isra'ila, A nan ya ba su izini su zauna a wurin, a cikin alfarwansu.
“Sa'ad da kuka rarraba ƙasar gādo, sai ku keɓe wa Ubangiji wani wuri domin ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), faɗinsa kuwa kamu dubu goma (10,000). Dukan yankin zai zama wuri mai tsarki.