Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 13:6 - Littafi Mai Tsarki

6 da dukan mazaunan ƙasar tuddai, tun daga Lebanon zuwa Misrefot-mayim har da dukan Sidoniyawa. Ni da kaina zan kore su a gaban jama'ar Isra'ila. Kai kuwa za ka raba wa Isra'ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 “Dukan mazauna kan yankunan tuddai daga Lebanon zuwa Misrefot Mayim, wato, dukan Sidoniyawa, ni da kaina zan kore su a gaban Isra’ilawa. Ka tabbata ka raba wa Isra’ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 13:6
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji kuwa ya ba da su a hannun Isra'ilawa, suka kuwa ɗibge su, suka runtume su, har zuwa Sidon Babba, da Misrefot-mayim, har zuwa gabashin kwarin Mizfa. Suka karkashe su ƙaƙaf.


to, sai ku tabbata Ubangiji Allahnku ba zai dinga korar al'umman nan daga gabanku ba, za su zama muku azargiya, da tarko, da bulala a kwiyaɓunku, da ƙayayuwa a idanunku. Da haka za ku ƙare sarai daga cikin kyakkyawar ƙasan nan da Ubangiji Allahnku ya ba ku.


Ga shi kuma, na rarraba wa kabilanku ƙasashen al'umman da suka ragu, da na waɗanda na shafe su tsakanin Urdun da Bahar Rum wajen yamma.


Za ku rarraba wa kanku gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar jefar kuri'a. Za ku ba babbar kabila babban rabo, ƙaramar kabila kuwa ku ba ta ƙaramin rabo. Inda duk kuri'a ta fāɗa wa mutum, nan ne zai zama wurinsa. Bisa ga kabilan kakanninku za ku gāji ƙasar.


Yanzu fa sai ka raba wa kabilai tara da rabi ɗin nan ƙasar ta zama gādonsu.”


Ka fito da kurangar inabi daga cikin Masar, Ka kori sauran al'umma, Ka dasa kurangar a ƙasarsu.


Ka dāge, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka yi jagorar wannan jama'a su mallaki ƙasa wadda na rantse zan ba kakanninsu.


Joshuwa kuma ya ci dukan biranen sarakunan nan, da dukan sarakunansu. Ya kashe su da takobi, ya hallakar da su ƙaƙaf kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarta.


Ubangiji Allahnku ne zai sa su gudu a gabanku, ya kore su daga ƙasar. Za ku mallaki ƙasarsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ