Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 13:3 - Littafi Mai Tsarki

3 daga Shihor da yake gabas da Masar zuwa iyakar Ekron a wajen arewa. Wannan ƙasa ta Kan'aniyawa ce. Akwai ƙasar sarakuna biyar na Filistiyawa da yake a Gaza, da Ashdod, da Ashkelon, da Gat, da Ekron, da ƙasar Awwiyawa,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Daga Kogin Shihor a gabashin Masar zuwa sashen Ekron a arewa, dukan wannan ƙasa ana lissafta ta a cikin ƙasar Kan’aniyawa, ko da yake tana a sashen da sarakuna biyar na Filistiyawa na Gaza, Ashdod, Ashkeloniyawa, Gat da Ekron; na Awwiyawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 13:3
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wace riba ka samu, har da ka tafi Masar, Don ka sha ruwan Kogin Nilu? Wace riba ka samu, har da ka tafi Assuriya, Don ka sha ruwan Kogin Yufiretis?


Al'umman da suka ragu a ƙasar su ne, birane biyar na Filistiyawa, da dukan Kan'aniyawa, da Sidoniyawa, da Hiwiyawa da suke zaune a Dutsen Lebanon, tun daga Dutsen Ba'alharmon har zuwa mashigin Hamat,


Haka nan kuma ya faru da Awwiyawa mazaunan ƙauyukan da suke kewaye da Gaza, wato su Kaftorawa waɗanda suka zo daga Kaftor, suka hallakar da su, suka zauna a wurinsu.)


Suka ce, “Wace irin hadaya za mu bayar?” Firistocin suka ce, “Sai ku yi marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa, gama annoba iri ɗaya ce ta same ku da sarakunanku.


Duk da haka jama'ar Isra'ila ba su kori Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa ba, amma suka yi zamansu tare da Isra'ilawa har wa yau.


'Ya'yan Ham su ne Kush, da Mizrayim, da Fut, da Kan'ana.


Shugabannin Filistiyawa, su biyar suka je wurinta suka ce mata, “Ki yi masa kirsa, don ki san dalilin irin ƙarfin nan nasa, da kuma yadda za mu yi maganinsa, mu ɗaure shi don mu rinjaye shi. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu da ɗari (1,100).”


Sa'ad da Filistiyawa suka ƙwace akwatin alkawarin Allah a Ebenezer, suka kai shi Ashdod.


Sa'an nan kuma Sulemanu ya yi biki na kwana bakwai, shi da dukan jama'ar Isra'ila. Mutane suka zo, tun daga Mashigin Hamat a arewa, har zuwa iyakar ƙasar Masar a kudu, suka hallara a gaban Ubangiji Allahnmu.


a hayin teku don su yi muku saye da sayarwa na hatsin da ake nomawa a Masar, su yi hulɗa da dukan sauran al'umma.


A wannan rana Ubangiji ya yi wa Abram alkawari ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis ke nan,


Sai suka aika, aka kirawo dukan sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka ce musu, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila?” Suka ce, “Sai a kai shi Gat.” Su kuwa suka kai shi can.


Sai suka kai akwatin alkawarin Allah zuwa Ekron. Amma da aka kai shi Ekron, sai mutanen Ekron suka fashe da kuka, suka ce, “Sun kawo mana akwatin alkawarin Allah na Isra'ila don ya kashe dukanmu.”


Haka fa, Dawuda ya tattara dukan Isra'ilawa wuri ɗaya, daga Shihor ta Masar, har zuwa mashigin Hamat domin a kawo akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ