Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 13:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Musa kuma ya ba rabin jama'ar Manassa rabon gādo bisa ga iyalansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Ga abin da Musa ya ba rabin kabilar Manasse, wato, wa rabin zuriyar Manasse, bisa ga iyalansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 13:29
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wannan shi ne yankin ƙasar, haɗe da garuruwa, da ƙauyuka, da aka ba mutanen kabilar Gad bisa ga iyalansu.


Yankin ƙasarsu ya bi daga Mahanayim, ya haɗa dukan Bashan, da dukan mulkin Og, Sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan,


Yankin Manassa yana kusa da yankin Naftali daga gabas zuwa yamma.


har kuma lokacin da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji kafin ku koma, to, za ku kuɓuta daga alhakinku a gaban Ubangiji da jama'ar Isra'ila. Wannan ƙasa kuwa za ta zama mallakarku a gaban Ubangiji.


Sai Musa ya ba mutanen Makir, ɗan Manassa, Gileyad, suka zauna ciki.


Sauran ƙasar Gileyad, da dukan ƙasar Bashan wadda take ƙarƙashin mulkin Og, wato dukan yankin ƙasar Argob.” (Duk dai yankin ƙasan nan wadda ake kira ƙasar Refayawa.) “Na ba da ita ga rabin kabilar Manassa.”


Saboda haka kuwa Manassa ya sami kashi goma banda ƙasar Gileyad da Bashan da yake hayin gabashin Urdun,


domin jikokin Manassa mata sun sami gādo tare da jikokinsa maza. Aka ba sauran mutanen kabilar Manassa ƙasar Gileyad.


Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manassa gādo a Bashan, sauran rabin kabilar kuwa Joshuwa ya ba su gādo tare da 'yan'uwansu a yammacin hayin Urdun. Sa'ad da Joshuwa ya sallame su zuwa gida, ya sa musu albarka,


Mutanen rabin kabilar Manassa suna da yawa, sun zauna a ƙasar, daga Bashan har zuwa Ba'al-harmon, da Senir, da Dutsen Harmon.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ