daga kuma Araba zuwa gabashin Tekun Kinneret da zuwa Tekun Araga, wato Tekun Gishiri, a wajen gabas ta hanyar Ber-yeshimot, da wajen kudu zuwa gangaren gindin Dutsen Fisga,
a hayin Urdun a kwari daura da Bet-feyor, a ƙasar Sihon, Sarkin Amoriyawa, mazaunan Heshbon, waɗanda Musa da Isra'ilawa suka ci da yaƙi sa'ad da suka fita daga ƙasar Masar.
Waɗannan duka su ne birane na kan tudu, da dukan masarautar Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya sarauci Heshbon. Musa ya ci shi da yaƙi da shugabannin Madayana, wato Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba, wato sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.