Dawuda yakan fita da mutanensa su kai wa Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa hari. Waɗannan su ne mazaunan ƙasar a dā, tun daga Shur har zuwa ƙasar Masar.
Abigail, matar marigayi, Nabal Bakarmele, ta haifa masa ɗansa na biyu, Kileyab. Ma'aka 'yar Talmai, Sarkin Geshur, ta haifa masa ɗansa na uku, Absalom.
Ya mallaki Dutsen Harmon, da Salka, da dukan Bashan, har zuwa iyakar Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa, da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon.
(Yayir na zuriyar Manassa ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma'akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawot-yayir.)
Taku ta ƙare, ku mazaunan gaɓar teku, ke al'ummar Keretiyawa! Ya Kan'ana, ƙasar Filistiyawa, Maganar Ubangiji tana gāba da ke, Za a hallaka ki har ba wanda zai ragu.