Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa na Ubangiji, Allah na Isra'ila, su ne gādonta, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.
Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, ɗan farin Isra'ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi. Waɗannan su ne iyalan kabilar Ra'ubainu.
Yanzu Ubangiji Allahnku ya ba 'yan'uwanku hutawa kamar yadda ya faɗa, yanzu dai sai ku koma, ku tafi gida a ƙasarku ta gādo wadda Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun.