Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 12:8 - Littafi Mai Tsarki

8 da ƙasar tuddai, da filayen kwaruruka, da kwarin Araba, da gangaren tuddai, da jejin, da Negeb, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Ƙasar ta haɗa da ƙasar kan tudu, filayen arewanci, Araba, gangaren Dutse, da jejin, da kuma Negeb, wato, ƙasashen Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 12:8
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta haka kuwa Joshuwa ya ci ƙasan nan duka, da ƙasar tuddai, da Negeb duka, da dukan ƙasar Goshen, da filayen kwari, da Araba, da ƙasar tuddai ta Isra'ila da filayen kwarinta,


Haka nan kuwa Joshuwa ya cinye dukan ƙasar tuddai, da Negeb, da filayen kwaruruka, da gangare, da sarakunansu duka, ba wanda ya ragu, amma ya hallaka su duka kamar yadda Ubangiji, Allah na Isra'ila ya umarta.


Sa'ad da dukan sarakunan da suke hayin Urdun, na cikin ƙasar tuddai, da na ƙasar kwari a gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon, wato sarakunan Hittiyawa, da na Amoriyawa, da na Kan'aniyawa, da na Ferizziyawa, da na Hiwiyawa, da na Yebusiyawa, suka ji wannan labari,


“Ku ji, ya Isra'ilawa, yau kuna kan haye Kogin Urdun, don ku kori al'ummai waɗanda suka fi ku yawa, sun kuwa fi ku ƙarfi. Suna da manyan birane masu dogon garu.


“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da kuke shiga ku mallake ta, zai korar muku da al'ummai da yawa, su Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, al'umma bakwai ke nan, waɗanda suka fi ku yawa, da kuma ƙarfi.


Mala'ikana zai wuce gabanku, ya bi da ku inda Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Kan'aniyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa suke, zan kuma hallakar da su ƙaƙaf.


don haka na sauko in cece su daga hannun Masarawa, in fito da su daga cikin wannan ƙasa zuwa kyakkyawar ƙasa mai ba da yalwar abinci, wato ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.


Abram kuwa ya ci gaba da tafiya, ya nufi zuwa wajen Negeb.


Akwai rashin jituwa kuma a tsakanin makiyayan dabbobin Abram da makiyayan dabbobin Lutu. Mazaunan ƙasar, a lokacin nan Kan'aniyawa da Ferizziyawa ne.


Joshuwa kuma ya ƙara da cewa, “Ta haka za ku sani Allah mai rai yana tsakiyarku, ba makawa kuwa zai kori Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Hiwiyawa, da Ferizziyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Yebusiyawa a gabanku.


Bayan wannan suka gangara kuma, suka yaƙi Kan'aniyawan da suke zaune a ƙasar tudu, da Negeb, da filayen kwari.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ