Ba sauran baƙin ciki ga wadda take shan azaba. Dā an ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zabaluna da na Naftali, amma nan gaba wannan jiha za ta sami daraja, tun daga Bahar Maliya, zuwa gabashin ƙasar a wancan sashe na Urdun, har zuwa Galili kanta, wurin da baƙi suke zaune.
A yankin ƙasar Issaka da na Ashiru, Manassa yana da waɗannan wurare, Bet-sheyan da ƙauyukanta, da Ibleyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Endor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta'anak da ƙauyukanta, da mazaunan Magiddo da ƙauyukanta, da sulusin Nafat.