Daga cikin rabon kabilar Naftali aka ba su birane uku, su ne, Kedesh ta Galili da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Hammon da wuraren kiwo nata, da Kartan da wuraren kiwo nata.
Hamada za ta raira waƙa da sowa don murna, Za ta zama kyakkyawa kamar Dutsen Lebanon, Da dausayi kamar filayen Karmel da Sharon. Kowa zai ga mafificiyar ɗaukakar Allah, Ya ga girmansa da ikonsa.
Akwai wani mutumin Mawon wanda yake da harka a Karmel. Mutumin mai dukiya ne ƙwarai, yana da tumaki dubu uku (3,000) da awaki dubu (1,000). Yana yi wa tumakinsa sausaya a Karmel.
Saboda haka suka keɓe Kedesh ta Galili a ƙasar tuddai ta Naftali, da Shekem ta ƙasar tuddai ta Ifraimu, da Kiriyat-arba, wato Hebron, ta ƙasar tuddai ta Yahuza.
Aka ba iyalan Merari na cikin Lawiyawa birane huɗu daga cikin rabon kabilar Zabaluna. Biranen ke nan, Yakneyam da wuraren kiwo nata, da Karta da wuraren kiwo nata, da Rimmon da wuraren kiwo nata, da Nahalal da wuraren kiwo nata.