Ƙasar na zaman banza, an gudu an bar ta. Jejin Lebanon ya bushe, kwarin Sharon mai dausayi ya zama kamar hamada, a Bashan kuma da a kan Dutsen Karmel sai ganyaye suke karkaɗewa daga itatuwa.
A wannan lokaci Isra'ilawa suka yi shiri su yi yaƙi da Filistiyawa, Isra'ilawa suka kafa sansaninsu a Ebenezer, Filistiyawa kuma suka kafa nasu a Afek.