Da Sarkin Arad, Bakan'ane, wanda yake zaune a Negeb, ya ji Isra'ilawa suna zuwa ta hanyar Atarim, sai ya fita ya yi yaƙi da Isra'ilawa, ya kama waɗansu daga cikinsu.
Ubangiji kuwa ya ji wa'adin Isra'ilawa, ya kuwa ba su Kan'aniyawa, suka hallaka su da biranensu ƙaƙaf. Don haka aka sa wa wurin suna Horma, wato hallakarwa.