Suka yi haka nan, suka kawo masa sarakunan nan biyar daga cikin kogon, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon.
Saboda haka zuriyarsu suka shiga, suka mallaki ƙasar Kan'ana. Ka rinjayi mutanen da suke zama a can. Ka ba jama'arka iko su yi yadda suke so Da mutane, da sarakunan ƙasar Kan'ana.