Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 10:2 - Littafi Mai Tsarki

2 sai ya tsorata ƙwarai, gama Gibeyon babban birni ce kamar ɗaya daga cikin alkaryai, har ma ta fi Ai girma, mazajenta duka kuwa ƙarfafa ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Shi da mutanensa suka ji tsoron wannan sosai, gama Gibeyon muhimmiyar birni ce, har ma kamar ɗaya daga cikin biranen sarauta, ya ma fi Ai girma, mazanta duka kuwa mayaƙa ne na ƙwarai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 10:2
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba mutumin da zai iya tsayayya da ku. Ubangiji Allahnku zai sa ƙasar ta firgita, ta ji tsoronku a duk inda kuka sa ƙafa, kamar yadda ya faɗa muku.


Suka kuma ce masa, “Hakika, Ubangiji ya ba da ƙasar duka a hannunmu, banda wannan kuma mazaunan ƙasar duka sun firgita saboda mu.”


Abu ne fa mai matuƙar bantsoro a fāɗa a cikin hukuncin Allah Rayayye.


sai dai matsananciyar fargabar hukunci, da kuma wuta mai tsananin zafi, wadda za ta cinye maƙiyan Allah.


Abin da mugun yake tsoro, shi yakan auko masa, amma adali yakan sami biyan bukatarsa.


Yowab kuwa ya yi yaƙi da Rabba ta Ammonawa, yana kuwa gab da cin birnin.


Dawuda ya ce wa Akish, “Idan na sami tagomashi a wurinka, ka ba ni wurin zama daga cikin garuruwanka na karkara domin in zauna a can. Gama me zai sa baranka ya zauna tare da kai cikin birni sarauta?”


Dukan mutanen duniya za su gane ku na Ubangiji ne, za su ji tsoronku.


Amma da mazaunan Gibeyon suka ji abin da Joshuwa ya yi wa Yariko da Ai,


A wannan rana ce zan fara sa al'ummai ko'ina a duniya su razana, su ji tsoronku. Sa'ad da za su ji labarinku, za su yi rawar jiki, su damu ƙwarai.’ ”


Sai suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Domin bayinka sun ji labari Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa ya ba ku ƙasar duka, ku hallaka dukan mazaunan ƙasar a gabanku, don haka muka ji tsoronku ƙwarai saboda rayukanmu, shi ya sa muka yi haka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ