Sai sarakunan duniya, da manyan mutane, da sarakunan yaƙi, da ma'arzuta, da ƙarfafa, da kuma kowane bawa da ɗa, suka ɓuya a kogwanni, da kuma a cikin duwatsu,
Za su lashi ƙura kamar maciji da abubuwa masu rarrafe, Za su fito da rawar jiki daga wurin maɓuyarsu, Da tsoro za su juyo wurin Ubangiji Allahnmu, Za su ji tsoronka.
Sa'ad da Isra'ilawa suka ga sun ƙuntata, gama an matsa su ƙwarai, sai suka ɓuya cikin kogwanni, da cikin ruƙaƙe, da duwatsu, da ramummuka, da kwazazzabai.
Sarakunan nan biyar na Amoriyawa, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon, suka tattaru da dukan rundunansu, suka haura, suka kafa wa Gibeyon sansani don su yaƙe ta.