Gibeyonawa dai suka aika zuwa wurin Joshuwa a zango cikin Gilgal cewa, “Kada ka yar da bayinka. Ka zo wurinmu da sauri, ka cece mu, ka taimake mu, gama dukan sarakunan Amoriyawa da suke zaune a ƙasar tuddai sun tattaru a kanmu.”
Ba a taɓa yin yini kamar wannan ba, ko kafin wannan yini, ko bayansa kuma, da Ubangiji ya saurari muryar mutum. Gama Ubangiji ya yi yaƙi domin Isra'ilawa.
Ya kuma kamo mutanen da suke cikin birnin, ya sa su su yi aiki da zartuka, da faretani, da gatura. Ya kuma sa su yi tubula. Haka Dawuda ya yi da dukan biranen Ammonawa. Sa'an nan Dawuda da dukan sojojinsa suka koma Urushalima.