Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 10:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Sai rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya, Har al'ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gābansu. Ai, wannan a rubuce yake a littafin Yashar. Rana dai ta tsaya a tsaka, ta yi jinkirin faɗuwa da misalin yini guda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Sai rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya, har sai da al’ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gābanta, kamar yadda aka rubuta a cikin littafin Yashar. Rana ta tsaya a sararin sama, ba tă fāɗi ba har kusan yini guda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 10:13
29 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Rana da wata sun tsaya cik a inda suke, A lokacin da kibanka masu haske suke wucewa fyu, Da lokacin walƙatawar hasken māshinka.


Ubangiji zai komar da inuwa baya da taki goma, bisa ga ma'aunin rana na sarki Ahaz.” Inuwa kuwa ta koma da baya daga fuskar rana har mataki goma.


Ba a taɓa yin yini kamar wannan ba, ko kafin wannan yini, ko bayansa kuma, da Ubangiji ya saurari muryar mutum. Gama Ubangiji ya yi yaƙi domin Isra'ilawa.


Sa'an nan Samson ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allah, ka tuna da ni, ina roƙonka, ka ƙarfafa ni sau ɗayan nan kaɗai, don in ɗauki fansa a kan Filistiyawa saboda idona biyu da suka ƙwaƙule mini.”


Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?


Rana da wata sun yi duhu, Taurari kuma ba su haskakawa.


Duniya takan girgiza saboda ita, Sammai sukan yi rawar jiki. Rana da wata sukan duhunta, Taurari kuwa sukan daina haskakawa.


Ku yabe shi, ku rana da wata, Ku yabe shi, ku taurari masu haskakawa!


Duk da haka muryarsu ta game duniya duka, Saƙonsu ya kai ko'ina a duniya. Allah ya kafa wa rana alfarwa a sararin sama,


Sai a ba kowane lardi fassarar dokar, don a yi shelarta ga dukan mutane, Yahudawa kuwa su yi shiri saboda wannan rana, domin su ɗau fansa a kan maƙiyansu.


Ya umarta a koya wa mutanen Yahuza wannan waƙa. (An rubuta ta a littafin Yashar.)


Wata zai duhunta, rana ba za ta ƙara haskakawa ba, domin Ubangiji Mai Runduna yake sarauta. Zai yi mulki a Urushalima a kan Dutsen Sihiyona, shugabannin jama'a za su dubi ɗaukakarsa.


Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Isra'ilawa suka ƙudura su yi yaƙi. Mutane suka sa kansu da farin ciki. Alhamdu lillahi!


Sa'ad da suke gudun Isra'ilawa suna a gangarar hawan Bet-horon, sai Ubangiji ya jefe su da manyan duwatsu daga sama, har zuwa Azeka, suka mutu. Waɗanda suka mutu ta ƙanƙarar duwatsu sun fi waɗanda Isra'ilawa suka kashe da takobi.


“Ka ɗaukar wa Isra'ilawa fansa a kan Madayanawa. Bayan ka yi wannan za ka mutu.”


Birnin kuwa ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, domin ɗaukakar Allah ita ce haskensa, Ɗan Ragon kuma fitilarsa.


Mala'ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi sulusin rana, da sulusin wata, da kuma sulusin taurari, har sulusin haskensu ya zama duhu, wato ba haske a sulusin yini, haka kuma a sulusin dare.


Da ya ɓamɓare hatimi na shida, na duba, sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, rana ta koma baƙa kamar gwado na gashi, gudan wata ya zama kamar jini,


Sai suka ta da murya da ƙarfi suka ce, “Ya Ubangiji Mamallaki, Mai Tsarki, Mai Gaskiya, sai yaushe ne za ka yi hukunci, ka ɗaukar mana fansar jininmu a gun mazaunan duniya?”


Za a mai da rana duhu, Wata kuma jini, Kafin Ranar Ubangiji ta zo, Babbar ranar nan mai girma.


domin ku zama 'ya'yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci.


Saboda haka aka faɗa a Littafin Yaƙoƙi na Ubangiji cewa, “Waheb ta cikin yankin Sufa, da kwaruruka na Kogin Arnon,


“Bayan tsabar wahalar nan, nan da nan sai a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba. Taurari kuma za su farfaɗo daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke sararin sama.


Rana za ta duhunta, Wata zai zama ja wur kamar jini, Kafin isowar babbar ranan nan mai bantsoro ta Ubangiji.


Hezekiya ya amsa, ya ce, “Ai, ya fi sauƙi inuwa ta yi gaba da taki goma da ta yi baya da taki goma.”


Allah yana da iko ya hana rana fitowa, Ko kuma ya hana taurari haskakawa da dare.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ