Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 1:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Ka dai dāge, ka yi ƙarfin hali ƙwarai, kana kiyaye dukan dokokin da bawana Musa ya umarce ka da su. Kada ka kauce musu dama ko hagu, gama da haka nan za ka arzuta cikin dukan harkokinka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 1:7
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za ka arzuta idan ka kula ka kiyaye dokoki da ka'idodi da Ubangiji ya umarci Musa saboda Isra'ila. Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karaya.


“Sai ku lura ku yi daidai bisa ga abin da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, kada ku kauce dama ko hagu.


Kada wannan littafin dokoki ya rabu da bakinka, amma zai zama abin da za ka yi ta tunani a kansa dare da rana domin ka kiyaye, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki, gama ta haka za ka yi albarka cikin hanyarka, ta haka kuma za ka yi nasara.


Ka rabu da mugunta ka yi tafiyarka sosai, kada ka kauce ko da taki ɗaya daga hanyar da take daidai.


Sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa bawansa, haka kuma Musa ya umarci Joshuwa, haka kuwa Joshuwa ya yi. Ba abin da bai aikata ba cikin dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa.


“Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku da shi, kada ku ƙara, kada ku rage daga cikinsa.


Sai Musa ya kira Joshuwa, ya yi masa magana a gaban dukan jama'ar Isra'ila, ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai wannan jama'a cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninsu. Kai ne za ka ba su ita gādo.


Saboda haka sai ku kiyaye, ku aikata dukan zantuttukan wannan alkawari don ku arzuta a cikin dukan abin da za ku yi.


idan kuma ba ku kauce zuwa dama ko hagu daga maganar da na umarce ku da ita yau ba, wato don ku bi waɗansu gumaka, ku bauta musu.”


A kan hanyar adalci nake tafiya, Rankai a kan hanyoyin gaskiya.


Ka yi abin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka. Ka yi biyayya da dokokinsa, da umarnansa, kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, domin ka yi nasara da dukan abin da kake yi da inda ka nufa duka,


Ya ɗibiya hannuwansa a kansa, ya keɓe shi kamar yadda Ubangiji ya umarta.


Bayan rasuwar Musa, bawan Ubangiji, Ubangiji ya ce wa Joshuwa ɗan Nun, wanda ya yi wa Musa aiki,


“Don haka fa, sai ku kiyaye dukan umarnan da na umarce ku da su yau domin ku sami ƙarfin da za ku haye, ku shiga, ku ci ƙasar da za ku mallaka,


Ashe, ban umarce ka ba? Ka dāge ka yi ƙarfin hali, kada ka firgita ko ka tsorata, gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai duk inda za ka.”


Domin haka sai ku yi ƙarfin hali ƙwarai, ku riƙe, ku aikata dukan abin da aka rubuta a littafin dokokin Musa, kada ku kauce dama ko hagu,


“Ina gab da rasuwa yanzu. Saboda haka, ka ƙarfafa, ka yi jaruntaka.


Ya yi abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji. Ya bi dukan halin kakansa, Dawuda, bai kauce dama ko hagu ba.


Amma ku sai ku yi ƙarfin hali, kada ku firgita, gama za a ba ku ladan aikinku.”


Ubangiji ya ce masa, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.”


Ya ce, “Ya kai, mutumin da ake sonka ƙwarai, kada ka ji tsoro, salama a gare ka, ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali!” Sa'ad da ya yi magana da ni, na sami ƙarfi na ce, “Yanzu sai shugabana ya yi magana, ka sa na sami ƙarfi.”


Kada ku ƙara, ko ku rage kome daga cikin abin da na umarce ku, amma ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, waɗanda nake umartarku da su.


Muku ƙwace ƙasarsu, muka ba Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, su gāda.


Ya mai da hankalinsa ga bin Ubangiji a kwanakin Zakariya, wanda ya koya masa tsoron Allah. Dukan lokacin da yake bin Ubangiji, Allah ya wadata shi.


Ka komo da mu, ya Ubangiji Allah Mai Runduna! Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ