Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 1:2 - Littafi Mai Tsarki

2 “Bawana Musa ya rasu, sai ka tashi ka haye Kogin Urdun, kai da dukan jama'an nan, zuwa cikin ƙasar da nake ba Isra'ilawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 “Bawana Musa ya mutu. Yanzu sai ka tashi tare da mutanen nan duka, ku yi shirin ƙetare kogin Urdun zuwa cikin ƙasar da zan ba su Isra’ilawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 1:2
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma ka umarci Joshuwa, ka ƙarfafa shi. Shi ne zai jagorar jama'ar nan, su haye, shi ne kuma wanda zai rarraba musu gādon ƙasar da za ka gani.’


Sai Musa ya kira Joshuwa, ya yi masa magana a gaban dukan jama'ar Isra'ila, ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai wannan jama'a cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninsu. Kai ne za ka ba su ita gādo.


Ubangiji ya ce, “Ga bawana, wanda na ƙarfafa, Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa. Na cika shi da ikona, Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.


“Ku shiga zango, ku umarci jama'a, ku ce, ‘Ku shirya wa kanku guzuri, gama nan gaba da kwana uku za ku haye Kogin Urdun don ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.’ ”


Bayan rasuwar Musa, bawan Ubangiji, Ubangiji ya ce wa Joshuwa ɗan Nun, wanda ya yi wa Musa aiki,


Ba haka nake magana da bawana Musa ba, na sa shi ya lura da dukkan jama'ata Isra'ila.


Nan fa, a ƙasar Mowab, Musa bawan Ubangiji, ya rasu kamar yadda Ubangiji ya faɗa.


Ubangiji ya ce masa, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.”


Zan ba ka, kai da zuriyarka a bayanka, ƙasar baƙuncinka, wato dukan ƙasar Kan'ana ta zama mallakarka har abada, ni kuwa zan zama Allahnsu.”


Ka riɓaɓɓanya zuriyarsu kamar taurarin sararin sama, Ka sa suka ci ƙasar, suka zauna cikinta, Ƙasar da aka yi wa kakanninsu alkawari za ka ba su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ