Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 9:7 - Littafi Mai Tsarki

7 ya ce masa, “Je ka, ka wanke ido a ruwan Siluwam,” wato aikakke. Shi ke nan sai ya je ya wanke ido, ya komo yana gani.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ya ce masa, “Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam” (kalman nan tana nufin “Aikakke”). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 9:7
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Makaho zai iya ganin gari, Kurma kuma zai iya ji.


Amma waɗansunsu suka ce, “Ashe, wanda ya buɗe wa makahon nan ido, ba zai iya hana wannan mutum mutuwa ba?”


Ya amsa ya ce, “Mutumin nan da ake kira Yesu ne ya cuɗa ƙasa ya shafa mini a idanu, ya ce mini, ‘Je ka Siluwam ka wanke ido.’ Na kuwa je na wanke, sai na sami gani.”


domin ka buɗe musu ido, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma mulkin Shaiɗan zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai, da kuma gādo tare da dukan tsarkaka saboda sun gaskata da ni.’ ”


Ya ce, “Saboda wannan jama'a ta ƙi natsattsen ruwan rafin Shilowa, suka yi ta rawar jiki a gaban sarki Rezin da sarki Feka,


Yakan ba makafi ganin gari. Yakan ɗaukaka waɗanda aka wulakanta. Yana ƙaunar jama'arsa, adalai.


Ko kuwa goma sha takwas ɗin nan da hasumiya ta faɗo a kansu, a Siluwam, ta kashe su, kuna tsammani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne?


Za ka buɗe idanun makafi, Ka kuma kwance waɗanda suke ɗaure a kurkuku masu duhu.


Sai Shallum ɗan Kolhoze, mai mulkin yankin Mizfa ya gyara Ƙofar Maɓuɓɓuga, ya gina ta, ya rufe ta, ya sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta. Ya kuma gina garun Tafkin Siluwam na gonar sarki, har zuwa matakan da suka gangaro daga Birnin Dawuda.


Ubangiji kuwa ya ce masa, “Wa ya yi bakin ɗan adam? Wa ya yi bebe ko kurma, ko mai gani ko makaho? Ko ba ni Ubangiji ba ne?


Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma a ƙarƙashin Shari'a,


Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.


kwa ce da wanda Uba ya keɓe, ya kuma aiko duniya, ‘Sāɓo kake,’ domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne’?


Yesu ya ce, “Na shigo duniyan nan ne don rarrabewa, domin waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda suke gani kuma su makance.”


Haske mai bayyana wa alummai hanyarka, Da kuma ɗaukakar jama'arka Isra'ila.”


Allah ya ce, “Kirawo mutanena a ɗakin shari'a. Suna da idanu, amma makafi ne, Suna da kunnuwa, amma kurame ne!


Idanunsu da kunnuwansu za su kasance a buɗe domin sauraron jama'a.


Makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, ana tsarkake kutare, kurame suna ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ