Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 9:39 - Littafi Mai Tsarki

39 Yesu ya ce, “Na shigo duniyan nan ne don rarrabewa, domin waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda suke gani kuma su makance.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

39 Yesu ya ce, “Saboda shari’a ce na zo duniya nan, saboda makafi su sami ganin gari, waɗanda suke gani kuma su makance.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 9:39
34 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Hukuncin kuwa shi ne, haske ya shigo duniya, amma mutane suka fi ƙaunar duhu da hasken, don ayyukansu mugaye ne.


Na zo duniya a kan ni haske ne, domin duk mai gaskatawa da ni kada ya yi zaman duhu.


domin ka buɗe musu ido, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma mulkin Shaiɗan zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai, da kuma gādo tare da dukan tsarkaka saboda sun gaskata da ni.’ ”


Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,”


Mai ƙin ɗan'uwansa kuwa, a duhu yake, a cikin duhu yake tafiya, bai san ma inda yake sa ƙafa ba, domin duhun ya makantar da shi.


“Ruhun Ubangiji yana tare da ni, Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara. Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru, In kuma buɗe wa makafi ido, In kuma 'yanta waɗanda suke a danne,


Domin yă haskaka na zaune cikin duhu, Da waɗanda suke zaune a bakin mutuwa, Domin ya bishe mu a hanyar salama.”


Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.


Saboda haka aka ce, “Farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu. Almasihu kuwa zai haskaka ka.”


Ga na ƙarshe ɗin, ƙanshin nan warin mutuwa ne, mai kaiwa ga hallaka, ga na farkon kuwa, ƙanshin rai ne mai kaiwa ga rai. To, wa zai iya ɗaukar nauyin waɗannan abubuwa?


Sai ya amsa ya ce, “Ko mai zunubi ne, ni ban sani ba. Abu ɗaya kam, na sani, dā ni makaho ne, yanzu kuwa ina gani.”


Ku kuna hukunci irin na duniya ne, ni kuwa ba na hukunta kowa.


Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa.


Ga shi fa, waɗansu da suke na ƙarshe za su zama na farko, waɗansu kuwa da suke na farko za su koma na ƙarshe.”


Nan take Yesu ya warkar da mutane da yawa daga rashin lafiyarsu da cuce-cucensu da kuma baƙaƙen aljannu. Makafi da yawa kuma ya yi musu baiwar gani.


Sai Saminu ya sa musu albarka, ya ce wa Maryamu uwar Yesu, “Kin ga wannan yaro, shi aka sa ya zama sanadin faɗuwar waɗansu, tashin waɗansu kuma da yawa cikin Isra'ila, Zai kuma zama alama wadda ake kushenta,


Makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, ana tsarkake kutare, kurame suna ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.


In kuwa idonka da lahani, duk jikinka sai ya cika da duhu. To, in hasken da yake gare ka duhu ne, ina misalin yawan duhun!”


Irin waɗannan mutane dakikai ne, har ba su san abin da suke yi ba. Sun rufe idanunsu da tunaninsu ga gaskiya.


Saboda haka sai ya ce mini in tafi in faɗa wa jama'a wannan jawabi cewa, “Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba. Kome yawan dubawar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.”


yana kuma yaudarar waɗanda suke a hanyar hallaka, muguwar yaudara, domin sun ƙi ƙaunar gaskiya har yadda za su sami ceto.


Ubangiji ya sa ku ku yi gyangyaɗi ku yi barci mai nauyi. Annabawa ne ya kamata su zama idon jama'a, amma Allah ya rufe idanunsu.


“Ɗan mutum, kana zaune a tsakiyar gidan 'yan tawaye da suke da idanun gani, amma ba sa gani, suna da kunnuwa na ji, amma ba sa ji, gama su 'yan tawaye ne.


Ƙyale su kawai, makafin jagora ne. In kuwa makaho ya yi wa makaho jagora, ai, duk biyu sai su faɗa a rami.”


Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari'a, yanzu ne kuma za a tuɓe mai mulkin duniyan nan.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ