32 Tun da aka fara duniya ba a taɓa jin wani ya buɗe idon wanda aka haifa makaho ba.
32 Ba wanda ya taɓa ji cewa an buɗe idanun wanda aka haifa makaho.
Ba wanda ya taɓa gani ko jin labarin wani Allah kamarka, wanda ya yi waɗannan ayyuka ga waɗanda suka sa zuciyarsu gare shi.
Sai aka yi ta walƙiya, da ƙararraki masu tsanani, da aradu, da wata babbar rawar ƙasa irin wadda ba a taɓa yi ba, tun da ɗan adam yake a duniya, gawurtacciyar rawar ƙasa ƙwarai da gaske.
Yadda tuntuni ya faɗa ta bakunan Annabawa nasa tsarkakan nan,
“Hakika ka sani tun daga zamanin dā, Sa'ad da aka fara sa mutum a duniya,
Mun sani Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma duk wanda yake mai bautar Allah, yake kuma aikata nufinsa, Allah yakan saurare shi.
Da mutumin nan ba daga Allah ya fito ba, da ba abin da zai iya yi.”
Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, wannan magana, ai, ba ta mai iska ba ce. Ashe, iska tana iya buɗe wa makaho ido?”