13 Sai suka kai wa Farisiyawa mutumin da yake makaho a dā.
13 Sai suka kawo mutumin da dā yake makaho wurin Farisiyawa.
Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi, amma saboda tsoron Farisiyawa, ba su bayyana ba, don kada a fisshe su daga jama'a.
Don dā ma, manyan firistoci da Farisiyawa sun yi umarni, cewa kowa ya san inda Yesu yake, ya zo ya faɗa, su kama shi.
Sai Farisiyawa suka ce wa juna, “Kun ga! Ba abin da muka iya! Ai, duk duniya tana bayansa.”
Suka ce masa, “Ina yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”
To, ran Asabar ne Yesu ya cuɗa ƙasar ya buɗe masa ido.