Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba, ko yadda ƙasusuwan jariri suke girma a mahaifar uwarsa, haka nan kuma ba ka san aikin Allah ba, wato wanda ya yi abu duka.
Ya amsa ya ce, “Mutumin nan da ake kira Yesu ne ya cuɗa ƙasa ya shafa mini a idanu, ya ce mini, ‘Je ka Siluwam ka wanke ido.’ Na kuwa je na wanke, sai na sami gani.”