Ga mutum biyu makafi zaune a bakin hanya. Da suka ji dai Yesu ne yake wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Ubangiji, ka ji tausayinmu, ya Ɗan Dawuda!”
Da mutanen garin suka ga mugun ƙwaron nan a makale a hannun Bulus, suka ce wa juna, “Lalle mutumin nan mai kisankai ne, kun ga ko da yake ya tsira daga bahar, duk da haka alhaki yana binsa sai ya mutu.”