Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 8:56 - Littafi Mai Tsarki

56 Ubanku Ibrahim ya yi farin ciki matuƙa ya sami ganin zamanina, ya kuwa gan shi, ya yi murna.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

56 Mahaifinku Ibrahim ya yi farin ciki sosai yă sami ganin ranata; ya kuwa gan ta, ya yi murna.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 8:56
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Waɗannan duka sun mutu cikin bangaskiyarsu, ba su kuwa sami abubuwan da aka yi musu alkawari ba, amma da suka tsinkato su, sai suka yi ta murna da ganinsu, suna kuma yarda su baƙi ne, bare kuma a duniya.


ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya za su sami albarka, saboda ka yi biyayya da umarnina.”


Suka amsa masa suka ce, “Ai, Ibrahim ne ubanmu.” Yesu ya ce musu, “Da ku 'ya'yan Ibrahim ne, da sai ku yi aikin da Ibrahim ya yi.


Hakika, ina gaya muku, annabawa da adalai da yawa sun yi ɗokin ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.


Ina gaya muku, annabawa da sarakuna da yawa suna son ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, suna kuma so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”


Waɗannan duka, ko da yake Allah ya shaide su saboda bangaskiyarsu, duk da haka, ba su sami cikar alkawarin ba,


Na san dai ku zuriyar Ibrahim ne, amma kuwa kuna neman kashe ni, don maganata ba ta shigarku.


Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, na faɗa muku, ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi da sunan Ubana, suke shaidata.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ