Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 8:47 - Littafi Mai Tsarki

47 Na Allah yakan saurari Maganar Allah. Abin da ya sa ba kwa sauraronta ke nan, don ku ba na Allah ba ne.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

47 Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 8:47
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kowa ya yi ƙari, bai tsaya a kan koyarwar Almasihu ba, Allah ba ya tare da shi ke nan. Wanda kuwa ya tsaya a kan koyarwar nan, yana da uba da Ɗan.


Sai Bilatus ya ce masa, “Wato ashe, sarki ne kai?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa, ni sarki ne. Domin haka musamman aka haife ni, don haka kuma musamman na shigo duniya, domin in shaidi gaskiya. Kowane mai ƙaunar gaskiya kuwa yakan saurari muryata.”


Ta haka sai a ga waɗanda suke 'ya'yan Allah, da kuma waɗanda suke 'ya'yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa.


Amma domin ina faɗar gaskiya, ba kwa gaskata ni.


Na san dai ku zuriyar Ibrahim ne, amma kuwa kuna neman kashe ni, don maganata ba ta shigarku.


Don me ba kwa gane maganata? Don ba kwa iya jimirin jin maganata ne.


Sai ya ƙara da cewa, “Shi ya sa na gaya muku, ba mai iya zuwa gare ni, sai ko Uba ya yardar masa.”


Ya ƙaunataccena, kada ka kwaikwayi mugun aiki, sai dai nagari. Kowa da yake aikin nagari na Allah ne. Mai mugun aiki kuwa bai san Allah ba sam.


Kowa da yake gaskata Yesu shi ne Almasihu, haifaffen Allah ne. Kowa yake ƙaunar mahaifi kuwa, yana ƙaunar ɗa kuma.


Mutane da yawa za su tsarkake kansu, su zama masu tsabta tsab tsab, amma mugaye ba za su gane ba, za su yi ta muguntarsu, amma masu hikima za su gane.


“Lalle hakika, ina gaya muku, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da matattu za su ji muryar Ɗan Allah, masu ji kuwa su rayu.


Wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi maganata ba, yana da mai hukunta shi, maganar da na faɗa, ita za ta hukunta shi a ranar ƙarshe.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ