Da wa zan yi magana don in faɗakar da shi, don su ji? Ga shi, kunnuwansu a toshe suke, su ji, Ga shi, maganar Ubangiji kuwa ta zama abin ba'a a gare su, Ba su marmarinta.
Saboda haka sai ya ce mini in tafi in faɗa wa jama'a wannan jawabi cewa, “Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba. Kome yawan dubawar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.”
Duk wanda yake da hikima, bari ya fahimci abubuwan nan. Duk wanda yake da ganewa, bari ya san abubuwan nan, Gama hanyoyin Ubangiji masu gaskiya ne, Masu adalci kuwa za su yi tafiya a cikinsu, Amma masu zunubi za su yi tuntuɓe a kansu.
Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta, Sun toshe kunnuwansu, Sun kuma runtse idanunsu, Don kada su gani da idanunsu, Su kuma ji da kunnuwansu, Su kuma fahimta a zuciyarsu, Har su juyo gare ni in warkar da su.’