Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 8:42 - Littafi Mai Tsarki

42 Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku da kun ƙaunace ni, domin daga wurin Allah na fito, ga ni nan kuwa. Ban zo domin kaina ba, shi ne ya aiko ni.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

42 Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 8:42
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba kuwa domin kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa, da kuma maganar da zan yi.


Wato ba ka gaskata ba cikin Uba nake, Uba kuma cikina? Maganar da nake faɗa muku, ba domin kaina nake faɗa ba, Uba ne da yake zaune a cikina yake yin ayyukansa.


Domin kuwa maganar da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa, sun kuma san hakika na fito daga wurinka ne, sun kuma gaskata kai ne ka aiko ni.


Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta san ka ba, amma ni na san ka, waɗannan kuma sun sani kai ne ka aiko ni.


Ubangiji Mai Runduna ya ce wa firistoci, “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bara kuwa yakan girmama maigidansa. Ni Ubanku ne, me ya sa ba ku girmama ni ba? Ni kuma Maigidanku ne, me ya sa ba ku ganin darajata? Kun raina ni, duk da haka kuna tambaya cewa, ‘Ƙaƙa muka raina ka?’


Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.


Mun duba, muna kuma ba da shaida, cewa Uba ya aiko Ɗan ya zama Mai Ceton duniya.


Ni na zo ne da sunan Ubana, ga shi, ba ku karɓe ni ba. In da wani zai zo da sunan kansa, shi za ku karɓa.


Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji yă zama la'ananne. Ubangijinmu fa yana zuwa!


Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa.


domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan.


Sa'an nan, sai ya nuna mini kogin ruwan rai, yana ƙyalli kamar ƙarau, yana gudana daga kursiyin Allah, shi da Ɗan Rago,


Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma a ƙarƙashin Shari'a,


Yesu ya amsa musu ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, domin na san inda na fito, da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ba, ko kuma inda za ni.


Yesu kuwa, da yake ya san Uba ya sa kome a hannunsa, ya kuma sani daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma,


Yanzu ne muka tabbata ka san kome, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.”


Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ