Ubangiji ya saukar mini da ikonsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, In warkar da waɗanda suka karai a zuci, In yi shelar kwance ɗaurarru, Da kuma 'yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku.
Amma duk mai duba cikakkiyar ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake aikatawa.
Ya ku 'yan'uwa, don 'yanci musamman aka kira ku, amma kada ku mai da 'yancin nan naku hujjar biye wa halin mutuntaka, sai dai ku bauta wa juna da ƙauna.
Haka Ubangiji ya ce, “Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba, Ku nemi hanyoyin dā, inda hanya mai kyau take, Ku bi ta, don ku hutar da rayukanku. Amma suka ce, ‘Ai, ba za mu bi ta ba.’
Sa'ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku cikin dukan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanar da ku al'amuran da za su auku.
Amma ku da kuke yi mini biyayya, ikon cetona zai fito muku kamar rana. Zai kawo warkarwa kamar hasken rana. Za ku fita kuna tsalle kamar 'yan maruƙan da aka fisshe su daga garke.
Za a yi babbar karauka a can, Za a kira ta, “Hanyar Tsarki.” Ba mai zunubi da zai taɓa bi ta wannan hanya, Ba wawayen da za su ruɗar da waɗanda suke tafiya can.
Jama'arsu za su ce, “Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji, Zuwa ga Haikalin Allah na Isra'ila. Za mu koyi abin da yake so mu yi, Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa. Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa, Daga Sihiyona yake magana da jama'arsa.”
Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.
Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya, da 'ya'yanta waɗanda nake ƙauna da gaske, ba kuwa ni kaɗai ba, har ma dukan waɗanda suka san gaskiya,