Saboda haka sai ya ce mini in tafi in faɗa wa jama'a wannan jawabi cewa, “Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba. Kome yawan dubawar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.”
Muna ta lalubar bango kamar makafi, muna ta lalubawa kamar marasa idanu. Da tsakar rana muke ta tuntuɓe, sai ka ce da almuru. A tsakanin waɗanda suke da cikakken ƙarfi, kamar matattu muke.
Akwai abubuwa da yawa da zan faɗa game da ku, in kuma hukunta. Amma shi wannan da ya aiko ni mai gaskiya ne. Abin da na jiyo daga gare shi kuwa, shi nake shaida wa duniya.”
Sai Yesu ya ce, “Sa'ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa'an nan ne za ku gane ni ne shi, ba na yin kome kuma ni kaɗai, sai dai Uba ya koya mini, haka nake faɗa.