18 Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.”
Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne.”
Ina faɗar abin da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abin da kuka ji daga wurin naku uba.”
sa'an nan kuma Allah ya haɗa shaidarsa, da tasu a kan ceton, ta alamu da abubuwan al'ajabi da mu'ujizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa.
Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.
Ni ne Makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni,
Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau kuwa shi ne mai ba da ransa domin tumakin.
Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo.
Lalle hakika, ina gaya muku, kowa ya kiyaye maganata ba zai mutu ba har abada.”
Sai suka ce masa, “Kai wane ne?” Yesu ya ce musu, “Daidai yadda na gaya muku.
Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,”
Ni da Uba ɗaya muke.”
Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu.
Duk wanda ya yi kisankai sai a kashe shi bisa ga shaidar shaidu, amma saboda shaidar mutum ɗaya ba za a kashe mutum ba.