17 A Attaurarku ma a rubuce yake, cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce.
17 A cikin Dokarku a rubuce yake cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce.
“Shaidar mutum ɗaya ba za ta isa a tabbatar, cewa mutum ya yi laifi ba, sai a ji shaidar mutum biyu ko uku, kafin a tabbatar da laifin mutum.
Bisa ga shaidar mutum biyu ko uku za a kashe shi, amma ba za a kashe mutum a kan shaidar mutum ɗaya ba.
Kowa ya yar da Shari'ar Musa, akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidu biyu ko uku.
In kuwa bai saurare ka ba, sai ka tafi da mutum ɗaya ko biyu, don a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.
Ashe kuwa, Shari'a ta zama uwargijiyarmu da ta kai mu ga Almasihu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya.
Wannan shi ne zai zama zuwana na uku a gare ku. Lalle ne kuwa a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.
Zan kuma bai wa mashaidana biyu iko su yi annabci kwana dubu da metan da sittin, suna a saye da tsummoki.”
Ku gaya mini, ku da kuke son Shari'a ta yi iko da ku, ba kwa sauraron Sharia ne?
Tun da yake muna yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa.
A kuma sa 'yan iska guda biyu, su yi ta zarginsa, su riƙa cewa, ‘Nabot ya zagi Allah da sarki.’ Sa'an nan ku tafi da shi, ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.”
An yi wannan kuwa domin a cika maganar da yake a rubuce a cikin Shari'arsu cewa, “Sun ƙi ni ba dalili.”
Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a Shari'arku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’?
Duk wanda ya yi kisankai sai a kashe shi bisa ga shaidar shaidu, amma saboda shaidar mutum ɗaya ba za a kashe mutum ba.