Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka kula da kyan tsarinsa, ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”
Yesu ya amsa ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina za su yi yaƙi kada a bāshe ni ga Yahudawa. Amma hakika, mulkina ba daga nan yake ba.”
Saboda haka ba ka da wata hujja, kai mutum, ko kai wane ne da kake ganin laifin wani. A yayin da kake ganin laifin wani, ai, kanka kake hukunta wa, don ga shi, kai mai ganin laifin wani, kai ma haka kake yi.
Saboda haka, a nan gaba ba mā ƙara duban kowane mutum bisa ga ɗabi'ar jiki kawai, domin ko da yake mun taɓa duban Almasihu bisa ga ɗabi'ar jiki, yanzu ba ma ƙara dubansa haka.