Yohanna 7:7 - Littafi Mai Tsarki7 Ba dama duniya ta ƙi ku, amma ni take ƙi, don na shaide ta a kan ayyukanta mugaye ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Duniya ba za tă iya ƙinku ba, amma ni take ƙi domin ina shaida cewa ayyukanta mugaye ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.