43 Sai kuma rabuwa ta shiga tsakaninsu a kansa.
43 Sai mutanen suka rabu saboda Yesu.
Saboda maganan nan fa, sai rabuwa ta sāke shiga tsakanin Yahudawa.
Saboda haka, waɗansu Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye Asabar.” Waɗansu kuwa suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin mu'ujizai haka?” Sai rabuwa ta shiga tsakaninsu.
Taro kuma suka riƙa maganarsa a raɗe, waɗansu na cewa, “Mutum ne nagari.” Waɗansu kuma na cewa, “A'a, ai, ɓad da jama'a yake.”
Amma mutanen birni suka rarrabu, waɗansu suka koma bayan Yahudawa, waɗansu kuma bayan manzannin.
Kuna tsammani na zo ne in kawo salama a duniya? A'a, ina gaya muku, sai dai rabuwa.
Domin na zo ne in haɗa mutum da ubansa gāba, 'ya da uwatata, matar ɗa kuma da surukarta.